Ahmad Shanawa ya Saki Sabuwar Bidiyo

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Nanaye dan asalin garin Jos Ahmad Shanawa da ake wa lakabi da baban chakwai, ya saki sabuwar fefen bidiyon wakar sa mai taken "Sarewar Kauna", wacce su ka yi tare da matashir jaruma Fati Abubakara.

Mawakin ya wallafa hoton shi da wannan jaruma ne a shafin sa na instagram tare da yi wa masoyan sa albishi da wannan sabuwar waka wacce ya ce za ta fito a ranar 12 ga watan Afrilu 2021 wato jiya Litinin kenan ana gobe azumin Ramadan zai fara.

Gidan Danger kashi na bakwai ya fito

Ahmad shanawa wanda ya yi wakoki sanannu da ake sauraron su a wajajan nishadi daban daban a arewaci da ma wasu sassa na kasan nan, kwanakin baya ya samu karuwa ta haihuwa inda mawakin ya samu ya mace a cikin watan Maris da ta gabata na shekarar 2021.

Kamar yadda aka san mawaki Ahmad Shanawa da salon wakokin rausayawa dai, akwai alamun wannan sabuwar ita ma kamar sauran salon wakokin sa ne sai dai sunan wakar na da alaka da soyayya, wanda wasu ke ganin za ta zo ne da salon da ba akai aka fi sanin Ahmad Shanawa ba.

Morell ya saki sabuwar waka a ranar zagayowar ranar haihuwar sa.

Leave your comment