Gidan Danger kashi na bakwai ya fito

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Sabon fim daga kwamfanin shirya finafinai a Kannywood mai dogon zango da aka fi sani da suna "Gidan Danger" kashi na bakwai ya fito a kafar YouTube.


Jarumi Yakubu Muhammad ne ya sanar da hakan a shafin sa na sada zumunci na Instagram, kare da albishir ga mabiya wannan fim mai dogon zango cewa, sabon kashi na wannan fim ya fito a YouTube din sa da kuma na Sani Danja. Wannan fim dai jarumi Yakubu ne ke bada umarni, yayin da shi kuma Sani Danja ke shiryawa.

Salim smart da Khairat sun sake yau sabuwar waka tare.

Alamu sun nuna, wannan fim ya fara shiga jerin finafinai da ake haska su a kafar YouTube wadan da su ke da tashin mabiya, kuma ana ganin nan da wani dan lokaci, wannan fim zai zama abun magana a arewacin Najeriya da ma wasu kasashen.

Yakubu Muhammad wanda ya ke cigaba da samun yabo daga mabiyan sa akan irin rawar da jarumin ya ke takawa musanman a sabbin finafinan sa na turanci, yanzu haka akwai finafinai manya guda biyu da jarumin ya fito a cikin su kuma ya nuna bajinta sosai a cikin su irin fin din Voiceless, da kuma Eagles wings.

UmmiZeezee ba ta mutu ba

Kuma wadan nan finafinai sun kai matsayin da za a kalle su a ko ina a duniya, wanda hakan cigaba ne ga jarumin da ma masana'antar Kannywood gabaki daya.

Rahama Sadau da Ali Jita sun nishadantar da mutane a Kano

Leave your comment