UmmiZeezee ba ta mutu ba

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A jiya Lagadi 11 ga watan Afrilu 2021 da musalin karfe biyu na rana ne aka tabbatar da mutuwar tsohuwar shahararriyar jaruma a masana'antar shirye finafinai ta Kannywood "Ummizeezee a dakin kawar ta a jahar Kaduna.

An wallafa labarin mutuwar jarumar ne a shafin ta na instagram bayan da aka daura hoton ta kwance ido rufe kuma daga ita sai kayan bacci. Inda kawar ta Khairat daga ungwar sarki a jahar Kaduna, ta yi wannan sanarwa tare da roka wa jarumar gafara da rahamar Allah.

Morell ya saki sabuwar waka a ranar zagayowar ranar haihuwar sa.

Cikin kankanin lokaci ne wannan labarin mutuwar Ummizeezee ya karede kafafan sadarwa daban daban, duba da a cikin makon daya wuce ne jarumar ta yi barazanar kashe kanta sakamakon yanayin kunci da ta ke ciki.

Jarumar ta shiga wani hali ne sakamakon wa su abubuwa uku kamar yadda ta baiyana da kan ta, wadan da su ka hadar da mutuwar mahaifin ta, mutuwar wani mutun da ta ke son shi sai kuma damfarar ta da aka yi a yan kwanakin baya.

Salim smart da Khairat sun sake yau sabuwar waka tare.

Daga lokacin ne Ummizeezee ta shiga halin damuwa da kuncin rayuwa, duk da dai kalaman yar uwarta Hasina Dan China na nuna cewa Ummizeezee ba ta mutu ba, tini hotunan ta su ka karede ko ina a yanar gizo ana roka mata gafarar ubangiji.

Har izuwa yanzu babu tabbacin mutuwar ta ko akasin hakan, amma alamu sun nuna babu cikakken gaskiyar wannan labari.

Amma za mu cigaba da bibiyar labarin dan tabbatar da gaskiyar lamarin.

Ahmad Delta ya saki sabuwar waka da salon bazata.

Leave your comment