Salim smart da Khairat sun sake yau sabuwar waka tare.

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Tin bayan fashewar da wakar "Zo mu sasanta" ta yi a wajan mabiya wakokin Hausa na salon Nanaye, Salim smart da Khairat sun sake yau sabuwar waka tare mai taken "Kaddarar masoya".

Fitaccen matashin mawaki kuma makadi Salim smart ne ya sheda wa masoyan sa fitowar wannan wakar a ta shafin sa na instagram jiya 11 gatan afrilu 2021. Inda ya tabbatar mu su da cewa, ya fitar da sabuwar waka tare da fitacciyar mawakiya Khairat Abdul yar garin Kaduna.

Tashar musulinci za ta fara haska finafinan Kannywood

Daga sunan wakar, ka na iya nazartar cewa wakar akan soyayya ne da kuma bangaran ta na daci ko rabuwa, sai dai idan mai karatu ya saurari wakar sai ya tambatar da ina wakar da dosa. Wannan ba shi ne karo na farko da mawakan biyu su ka yi waka tare ba tin bayan Zo mu sasanta, amma ana ganin wannan wakar ta fito ne a lokacin da ba a yi tsanmani ba.

An fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a salon waka.

Duba da yadda a kwanakwanan nan ne mawakan biyu su ka fitar da sabbi wakoki a mabanbantan lokuta kuma ana tsaka da sauraran su ne wannan sabuwar wakar ta sako kai.

Idan mai sauraro zai tuna, Salim smart ya saki wakar "Mai kike nufi ne" tare da Fresh Emir, sai kuma ita khairat ta fitar da bidiyon wakar Alkawari tare da sako Hamisu Breaker a fitowa ta musanman.

Mawakiya Khairat ta fitar da bidiyon ta da Hamisu Breaker

Leave your comment