Mawakiya Khairat ta fitar da bidiyon ta da Hamisu Breaker

Picture source : Khairat instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar matashiyar mawakiya yar yayi Khairat Abdul yar asalin jahar Kaduna ta saki sabuwar fefen bidiyon ta mai taken "Alkawari" tare da mawaki dan yayi Hamisu Breaker a cikin bidiyon na ta a matsayin saurarin da ta ke wakewa.


Khairat ta fitar da wannan wakar ne a cikin farkon watan Afrilu 2021, daidai da lokacin da ake ganin sabbin wakoki na fitowa daga masana'antar musanman daga mawaka maza. Ta sanar da fitar bidiyon ne ta shakukan ta na sadar zumunci, tare da daura dan kadan daga cikin bidiyon wakar ta, "Alkawari".

Khairat wacce haihuwa da tasowar garin Kaduna ne, ta samu daukaka ne a cikin wakar fim din Mansoor mai taken "Abun da ke raina" da su ka yi tare da mawaki Abdul D One. Daga nan kuma ta dada bunkasa ta hanyar wakokin finafinai da dama da aka yi da ita.

Ko a kwanakin baya, mawakiyar ta fito a wakar Salim Smart mai taken "Zo mu sasanta", kuma ana ganin ita ce ma sanadiyar fashewar wakar, saboda yadda salon ta da kalaman ta a cikin wakar ya burge masu sauraro da dama.

Ahmad Delta ya saki sabuwar waka da salon bazata.

A cikin matasan yan mata a masana'antar fim ta Kannywood ma su wako da amshi, za a iya cewa muryar Khairat aka fi amfani da ita a yawancin wakokin kuma ana ganin ta yi dabara da ta fara fitowa a cikin bidiyon wakokin ta na kan ta dan ita ma duniya ta san fuskar ta.

Umar M. Shareef ya bude wuta a shekarar 2021

Leave your comment