Umar M. Shareef ya bude wuta a shekarar 2021

Picture source : Instagram account 

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawaki kuma jarumi a Kwnnywood dan asalin jahar Kaduna Umar M. Shareef ya bude wuta a shekarar 2021 da irin aiyukan da mawakin ke fitarwa babu kakkautawa a yan kwanakin nan. Cikin satuttukan da su ka gabata ne mawakin ya fitar da fefen bidiyon wakar sa mai taken "Lagwada" wacce makadi selebobo ya yi aikin ta kuma daracta Bash M. ya yi aikin bifiyon ta.

Jarumi Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau

Sai gashi babu shiri Umar M. Shareef ya sake fitar da wata sabuwar wakar tare da bidiyon ta mai taken "Mafarki". Bidiyon wanda babban mai bada umarni musanman a irin wakokin Nanaye wato Sunusi 442 ya bada umarni, ya samu kyakkyawar labari tare dauka mai burgewa. Kuma jaruma Mummy Gombe ce ta fito a cikin bidiyon wakar.


Umar M. Shareef bayan da ya wallafa wani bangare na bidiyon a shafin sa na instagram, ya bukaci masoyan sa da su garzaya shafin sa na YouTube dan kallon wannan sabuwar wakar ta sa, tare albishir ga masoyan sa akan wannan sabuwar waka da ya fitar.

Mawaka sun yi wa Ado Gwanja bazata

Umar M. Shareef har yanzu dai na cigaba da kasancewa da kambun sa na daya daga cikin mawaka biyu a tarihin masana'antar fim ta Kannywood da mawakan Nanaye wanda su ka haura shekara uku su na tashe kuma har yanzu ana yi da su kamar a da. Wannan wakar za ku same ta a man'hajar mu ta Mdundo dan nishadantuwa da ita.

Da ba dan ni ba ne na yi, da na kai mawakin da ya yi wakar Ta na so kara kotu. "Mr Ladagoma".

Leave your comment