Jarumi Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau

Picture source : Umar Gombe instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin fitattun jarumai a masana'antar Kannywood kuma mai bada gudunmawa a tafiyartar da masana'antar a zamanance wato Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau Alhamis 5 ga watan Afrilu 2021.

Jarumin wanda ya wallafa hotunan sa sabbi da ya dauka adalilin wannan rana a shafukan sa na sadarwa, ya sanar da hakan ne a karkashin wadan nan hotunan da ya wallafa. Inda jarumai yan uwan sa da dama su ka wallafa hotunan sa a na su shafukan tare da taya shi murna da adduar fatan alheri da kuma karin shekaru ma su albarka da anfani.

Morel ya saki sabuwar bidiyon wakar sa

Umar Gombe wanda ya na daga cikin jarumai ma su jin harshen turanci kuma su ke finafinai irin na harshen turanci a masana'antar Kannywood, musanman irin finafinan kwamfanin Jammaje irin su "In search of the king".

Ya na daya daga cikin jaruman da ake ganin har yanzu manana'antar Kannywood bata san mahimmancin su yadda ya kamata ba, duba da yadda su ke da tarin ilimi da kuma kwarewa a harkar finafinai a zamanance, kuma ana ganin idan aka baiwa irin su karin damanmaki wajan gudanarwa da shawarwari akan manana'antar, za a kai wani mataki da zai kawo wa manana'antar cigaba nan kusa.

Mawaki Shanawa ya na shirin sakin sabuwar bidiyo

Muma daga nan muna yi wa jarumi Umar Gombe murnar wannan rana ta zagatowar ranar haihuwar sa tare mai fatan alheri.

Jarumi Zango ya fito a cikin fim din "Gidan Badamasi" zango na uku

Leave your comment