Jarumi Zango ya fito a cikin fim din "Gidan Badamasi" zango na uku

Picture source : Falalu A. Daurayi

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararran jarumi kuma mawaki a masana'antar Kannywood da Hausa Hip Hop Adam A. Zango ya fito a cikin fim din "Gidan Badamasi" zango na uku.

A yayin da ake dakon fara ganin cigaban fim mai dogon zango na Gidan Badamasi kashi na uku, sai ga karin sababbin fuskokin jarumai maza da mata da babu su a cikin zangon farko da na biyu, cikin su kuwa har da jarumi Adam A. Zango.

Mawaki Abdul D one ya na shirin sakin sabuwar bidiyo.

Jarumin wanda ya fito a matsayin mai lefi kuma daurarre a gidan gyaran hali wato kurkuku, ya fito ne a cikin fim din da suna "Birema Icen Kabari". Wasu daga cikin jarumai a wannan fim sun hada da Mustapha nabaraska a matsayin "Bazooka" da Nura dan dolo a matsayin "Dan kwanbo", da Aminu Mirror a matsayin "Zaidu". Duk a cikin wannan sabon zango na fim din "Gidan Badamasi".

Mawaki Musa Africa ya fitar da sabuwar kundin sa

Fitar Adam Zango cikin wannan fim zai kara wa fim din daukaka da karin yan kallo sosai daga dukkan alamu, musanman yadda aka san harumi zango da take rawa a irin wannan matsayi na mai lefi. Kamar yadda ya yi a fin din sa na "Basaja" da kuma fim din "Hindu".

Adam Zango wanda ake wa ganin na biyu a shahara da daukaka cikin jaruman Kannywood a tarihi bayan jarumi Ali Nuhu, ya yi finafinai daukakkaku da dama kuma jarumi ne da ya yi kaurin suna wajan shiga matsala ko rigima da sauran abokan sana'a a masana'antar.

Jarumin Lawan Ahmad ya samu karuwa ta haihuwa

Mawaki Salim Smart ya saki sabuwar waka

Leave your comment