Mawaki Abdul D one ya na shirin sakin sabuwar bidiyo.
6 April 2021
Picture source : Abdul D One official instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararren mawakin Nanaye kuma matashin jarumi a masana'antar Kannywood Abdul D One ya saki sabuwar waka a yan kwanakin nan, mai taken "Ko za a fasa", kuma a halin yanzu mawakin na kokarin fitar da fefen wannan sabuwar waka a cikin yan kwanakin nan ma su zuwa.
Mawakin ya wallafa hotuna ne da aka yi su a cikin bidiyon waka kuma ya daura su a shafin sa na instagram. Inda masoyan sa ke nuna farin cikin su da ganin wannan hotuna.
Mr 442 ya saki sabuwar bidiyon wakar sa
Akwai alamun an yi wannan bidiyon ne a jahar Legas bakin taku, kamar yadda hotunan da aka wallafa ke nunawa. Abdul D One dai ya juma ya na wakoki a masana'antar Kannywood, amma daukakar sa ta zo ne a cikin wakar fim din Mansoor da ya yi tare da mawakiya Khairat mai taken "Abin da ke raina". Bayan da mawaki Umar M. Shareef ya hau wakar a cikin fim din, sannan hirar da kwamfanin FKD ta hada wa mawakan ta kara taimakawa wajan sanuwar su ga masoyan wakoki da finafinan Kannywood.
Duk da wasu masoyan na ganin kamar muryar mawaki Abdul D One ya na kama da ta Umar M. Shareef, musanman alakar da ke tsakanin mawakan biyu na uban gida da yaron sa, wato Umar M. Shareef shi ne uban gidan mawaki Abdul D One, wanda banda waka kuma makadi ne shi.
Abdul ya yi wakokin finafinai da dama kuma ya yi wadan da ba na fim bane su ma. Kuma ya na daga cikin mawakan da ake ganin za su gaji irin su Umar M. Shareef da Nura M. Inuwa a fagen Waka.
Leave your comment