Mr 442 ya saki sabuwar bidiyon wakar sa
6 April 2021
Picture source : Madox Tbb official instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen matashin mawaki dan garin Zaria dake jahar Kaduna Mr 442 ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Soro soke" a yau 1 ga watan Afrilu 2021.
Mawakin ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram tare da sanar wa masoyan sa cewa wannan wakar ta "Soro soke" tiny ya sake ta a shafin sa na YouTube kuma ya na kira da su je su kalla.
Jarumin Lawan Ahmad ya samu karuwa ta haihuwa
Mr 442 wanda a makon da ta shige ne na karshen watan Maris su ka fitar da wakar "Sai Monday" tare da mawaki Madox dan asalin jihar Kano, wanda su ka yi fada da shi a kwanakin baya kafin daga bisani su shirya tsakanin su. Haka zalika Mr 442 ya fito a sabuwar wakar Deezell mai taken "No boyfriend" tare wasu mawakan mutun biyar da Deezell ya saka a cikin wakar.
Makadi Nexcezz Beatz ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
Mr 442 na daga cikin mawakan da ake sauraron su a shafukan sada zumunci da dama a halin yanzu, kuma daga dukkan alamu a shekarar nan mawakin zai ba da mamaki a masana'antar Hausa Hip Hop. Duba da irin wakokin da mawakin ke fitarwa akai akai.
Daracta MSK ne ya yi aikin wannan bidiyon, kuma mawaki Madox Tbb ya yi fitowar musanman a cikin bidiyon. Daga nan Mdundo mu na cigaba da bibiyar mawaki Mr 442 dan sanin wani abu sabo zai fita daga wajan mawakin dan mu sanar wa mabiyan mu.
Leave your comment