News on Kasheepu new song with Nura M. Inuwa

Picture source : Kasheepu official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren makadin wakokin Hausa na salon Nanaye kuma manaja ga tauraron mawaki Hamisu Breaker wato Kashif Amjad wanda aka fi sani da "Kasheepu" (kasheepun kida), ya saki sabuwar waka mai taken "Mu gudu tare", wanda ya yi tare da fitaccen mawakin Kannywood Nura M. Inuwa.

Wakar ta fita ne yau Laraba 31 ga watan Maris 2021, wacce ita ce rana ta karshe a cikin wannan watar da mu ke ciki. Kasheepu ya shanmashi mabiya wakokin Hausa da dama da su ka wayi gari da wannan wakar tare da Nura M. Inuwa, sabanin zaton su zai yi wakar ne tare da mawakin ka wato Breaker. Musanman idan aka yi la'akari da alakar sa da Breaker da kuma yadda mawakin ke kan ganiyar tashen sa a halin yanzu.

Wani abun da ya kara jan hankalin mabiya wakokin Nanaye shi ne yadda da yawa daga cikin su ba su san cewa makadi Kasheepu yana waka ba, domin da kida su ka san shi. Duba da yadda shi ma kasheepun ya ke kan ganinyar sa na tashe a cikin jerin makada fitattu da ake ji da su a kasar Hausa a halin yanzu.

Wannan wakar dai an fitar da ita ne a karkashin kwanfanin makadin mai suna "Amjad Record", inda kuma shi kasheepun ne ya yi aikin wannan wakar gabaki dayan ta.

Tini wannan wakar ta fita a man'hajoji daban daban na sauke wakoki kuma masoya na ta baiyana ra'ayoyin su akan wannan wakar.

Leave your comment