Makadi Nexcezz Beatz ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
1 April 2021
Picture source : Nexcezz facebook page
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen makadi kuma mawakin Hausa Hip Hop daga jahar Kano Nexcezz Beatz wanda shi ne shugaban kwamfanin sa mai suna Nexcezz Beatz Inc. ya yi bikini zagayowar ranar haihuwar sa jiya Talata 30 ga watan Maris 2021.
Mawakin ya wallafa hotunan sa ne tare da iyalan sa a shafukan sa na sada zumunci, tare da sanar wa abokan arziki da masoyan sa cewa su taya shi murnar zagayowar wannan rana ta haihuwar sa.
Nexcezz wanda ya sanu a matsayin makadi a lokacin da ya ke kida a karkashin kwanfanin Spotlite da ke kan titin zoo road dake garin Kano, ya yi wa fitattun mawakan Hausa Hip Hop da dama ayyuka wadan da su ka yi tashe irin su wakar Jallabiya ta Hazy D-Star, Ladagoma ta Dabo Daprof, Katako ta Billy-O, Babban managa ta K. Arrows, Taka rawa ta marigayi Lil Amir, Kano city ta Deezell da dai sauran su.
Makadin mawakin wanda a cikin watan nin baya ne ya fitar da wata kundin waka mai dauke da wakoki har guda sittin da daya (61), wanda acikin ta ya saka mawaka da dama, ya fitar da wata sabuwar waka a kwanan nan mai taken Champion tare da mawakiyar R and B mazauniyar garin Abuja wato Sals fateetee.
Mawaka da dama ne jiya su ka wallafa hotunan makadi Nexcezz a shafukan su na sada zumunci dan taya shi murnar zagayowar wannan ranar ta haihuwar sa.
Nexcezz na daga cikin fitattun makadan zamani na Hausa Hip Hop da jahar Kano ne alfahari da su duba da irin mawaka kanana da manya da su ke aiki tare da shi wanda ku ma wasu daga cikin kananan mawakan ke karkashin kulawar makadin a matsayin mai tallafa wa harkar su ta waka.
Daga nan Mdundo muna wa makadi Nexcezz murna da fatan alheri.
Leave your comment