Jarumin Lawan Ahmad ya samu karuwa ta haihuwa
6 April 2021
Photo credit : Lawan Ahmad instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen Jarumin kannywood kuma dagoran shahararren fim mai dogon zango "Izzar So" Lawan Ahmad ya samu karuwar haihuwa ta ya mace a ranar talata 30 ga watan Maris 2021.
Jarumin ya sanar da haka ne a shafin sa na instagram bayan da ya wallafa hoton sa da na sabuwar jaririyar ta sa tare da sanar wa masoyan sa abun alherin da ya same shi, inda ya fara da yi wa Allah godiya tare da baiyana farin cikin sa akan wannan rabo da Allah ya ma sa.
Mawaki Salim Smart ya saki sabuwar waka
Sama da masoya dubu daya ne su ka yi wa jarumin fatan alheri da san barka a karkashin wannan hoto da ya wallafa. Inda kuma mawaka da jarumai da dama ne a masana'antar su ka taya shi farin ciki ta hanyar wallafa hoton jarumin da jaririyar sa.
Lawan Ahmad wanda ya ke da mabiya mutun dubu dari takwas da hamsin da biyu (852K), yayin da shi kuma yake bin mutun dubu daya da tamanin da biyar (1085).
News on Kasheepu new song with Nura M. Inuwa
Jarumin kafin fitowar fim din sa ta "Izzar So", ya fito a manyan finafinai a masana'antar Kannywood kuma ya shahara a fagen soyayya a finafinan da ya ke fitowa a ciki kafin ya fara fim din sa na Izzar So wacce ta karade ko ina a yan watannin nan da su ka wuce. Kuma har yanzu ana cigaba da yayin wannan fim mai dogon zango.
Daga nan Mdundo mu na cigaba da bibiyar jarumi Lawan Ahmad, dan sanin wani abu sabo zai fito daga wajan sa dan mu sanar wa mabiyan mu.
Mawakin R and B Sonikman ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
Makadi Nexcezz Beatz ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
Leave your comment