Mawaki Salim Smart ya saki sabuwar waka
6 April 2021
Picture source : Fresh Emir's official instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Matashin mawaki a masana'antar Kannywood mai salon wakokin Nanaye Salim Smart ya saki sabuwar waka yau daya ga watan Afrilu 2021 mai taken "What do you mean?" wato a hausance (Mai kike nufi?), tare da fitaccen matashin mawakin hima a masana'antar Hausa Hip Hop wato "Fresh Emir", aku mai bakin magana.
News on Kasheepu new song with Nura M. Inuwa
Mawakin ya wallafa hoton artwork na wannan wakar ne a shafin sa na instagram tare da sanarwar fitowar wannan waka ta su, yayin da shi ma Fresh Emir ya wallafa wannan hoton tare da yi wa masoyan sa albishir da wannan waka da ya fito a ciki.
Salim Smart wanda ya yi wakoki da dama a yan shekarun nan da su ka yi tashe irin su wakar "Zo mu sasanta" kuma har ake ganin kamar akwai yuwar ya zama daya daga cikin mawakan da za su gaji irin su Hamisu Breaker daga jahar Kano.
Makadi Nexcezz Beatz ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
Salim Smart bayan waka da aka san shi da shi, ya kasance makadi ne kuma da salon zamani irin wakokin kasar Tanzania da Ethiopia.
Tini masoyan mawakan su ke ta baiyana ra'ayin su akan wakar ta Salim smart tare da Fresh Emir kuma daga dukkan alamu wannan wakar zata nishadantar, duba da yadda matasan biyu su ke da kokari wajan aiki mai kyau da ma'ana.
Leave your comment