MSK ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
31 March 2021
Picture source : Musab Hausatop official instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop daga jihar Kano kuma gwararren mai bada umarni tare da daukan bidiyon waka MSK da ake wa lakabi da Sir MS ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a ranar Asabar 27 ga watan Maris 2021 a cikin farin ciki da annushuwa.
An wayi gari ne da hotunan daracta MSK ne, a shafukan sada zumunci daban daban na manya da kananan mawaka da jarumai daga masana'antar Kannywood da kuma na Hausa Hip Hop, inda su ke mai murnar zagayowar yanar haihuwar sa tare da masa adduar dacewa da kuma karin cigaba a rayuwa.
MSK, wanda daga lokacin da ya fara harkar daracta izuwa yanzu ya yi wa manyan mawaka bidiyo daban daban cikin su akwai wadan da ya yi su a yan shekarun nan irin su bidiyan Ado Gwanja, Lilin Baba, Hazy D-Star, Mr 442, Fresh Emir, da dai sauran su.
MSK ya kara sanuwa ne a masana'antar Hausa Hip Hop da na Kannywood, bayan da fitatten yaron mawaki Lil Amir ya rasu kuma da dama alokacin su ka san cewa MSK da Abba Manager ne su ke tallafawa tare da gudanar da harkokin Lil Amir kafin rasuwar sa a sanadiyar hatsarin mota da ta faru da su a lokacin da su ke kan babur mai kafa biyu.
Mu na yi wa MSK fatan alheri da karin shekaru ma su albarka nan gaba.
Leave your comment