Matashin mawaki Dj Speysh na shirin sakin sabuwar waka
1 April 2021
Picture source : YK Designer's official instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Matashin mawaki Dj speysh dan jahar Kano na shirin saki sabuwar wakar sa mai taken "We made it" a ranar hudu ga watan Afrilun 2021 da zamu shiga. Mawakin ya yi wannan sanarwar ne shekararan jiya a shafukan sa na sada zumunci, inda ya baiyana cewa wannan sabuwar wakar ya yi ta ne tare da mawakan Hausa Hip Hop biyu da ake ji da su a jahar Kano wato Aj D incredible da kuma young Gee.
Dj Speysh wanda a shekaru biyu da su ka gabata ya yi wakoki guda biyu wadan da ya sanya mawaka banya a cikin su irin su Ado Gwanja, Dabo Daprof, Sonikman da sauran su. Wakoki su ne Sarauniya da kuma My Side. Wanda daga lokacin ne matashin mawakin ya kara sanuwa.
Speysh wanda graphic designer ne ya yi wa mawaka da dama artwork a masana'antar Hausa Hip Hop kuma ya na daya daga cikin kananan mawaka ma su Jama'a a masana'antar ta Hausa Hip Hop. Wannan sabuwar wakar dai zata fito ne a ranar Lahadi 4 ga watan 4, kuma ana sa ran zata samu karbuwa kamar sauran wakokin da mawakin ya fitar a baya.
Leave your comment