Mawakin R and B Sonikman ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa
1 April 2021
Picture source : Sonikman official instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen mawakin R and B, makadi kuma mai bada umarni tare da daukan bidiyo Sani Suleiman wanda aka fi sani da Sonikman ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a jiya Talata 30 ga watan Maris 2021.
Mawakin ya yi dan kwaryakwaryar taron murnar wannan ranar a studio din Vocal sounds studio dake jahar Kano, inda anan mawakin ke da zama. Anyi wannan taron taya murna ne da yanma bayan sallar magariba zuwa isha'i. Cikin wadan da su ka halarci wannan taro sun hadar da fitattun mawaka maza da mata irin su Dabo Daprof Mister Ladagoma, A-styl dbd, Daracta Aminu Bala Mugu, Y Malam, YK Designer, Aminu Gulu, Abba Vocal, Swagger Vocal, M Khan, Queen Zeeshaq da kuma Jamila Jamcy da dai sauran su.
Bayan an yanka cake, wanda mawaki Dabo Daprof ya jagoyanci bikin, sai aka karkere taro da abinci da sha tare da rabon cake ga mahalta wannan taro.
Sonikman na daya daga cikin mawaka yan asalin jahar Kano ma su tarin baiwa da basira a bsngare daban daban. Cikin abubuwan da Sonikman ya yi suna da su a masana'antar Hausa Hip Hop da na Kannywood sun hadar da : Waka, kida, editing na bidiyo, daukan bidiyo, bada umarni, graphic design, zane, Animation (zanen cartoon) da dai sauran su.
Mawakin ya samu masoya da abokan arziki da dama da su ka mai fatan alheri a shafukan su na sada zumunci, inda shi ma ya marar mu su da sakon godiya tare da jinjina ga kowa da kowa.
Mu ma daga nan Mdundo mu na yi wa Sonikman fatan karin shekaru ma su albarka.
Leave your comment