Mawaki Musa Africa ya fitar da sabuwar kundin sa

Picture source : Dj Ab official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Katsina da aka sani da "Musa Africa" ya saki sabuwar kundin wakokin sa da ya yi wa take "Musa in black " (M. I. B) a cikin makon nan da ta gabata na watan Maris 2021.

Mr 442 ya saki sabuwar bidiyon wakar sa


Kundin da ke dauke da wakoki har guda shida (6) wanda ya saki a matsayin gajeriyar kundin wakoki da a ke wa lakabi da (EP), wato Extended play kenan a turance. Kuma a cikin kundin na "Musa in black ", mawaki Musa ya gaiyaci manyan mawakan Hausa Hip Hop irin su Dj Ab a cikin waka ta farko mai suna "Kina juya ni", sai Deezell a cikin waka ta biyu mai taken "Skikenan", sai mawaki Morel a cikin waka ta shida tare da YoungCee mai taken "Kings of the north" da kuma Kheengs a cikin waka ta biyar mai taken "Ke nike kauna".

Ragowar wakokin da mawakin bai yi da wasu ba a cikin kundin wanda shi kadai ya yi su, akwai waka ta uku mai suna "Zobe" da kuma waka ta hudu mai taken "Ta gan ni". A cikin makidan da su ka yi aikin wannan kundin na "Musa in black " sun hada da
Mega mix a waka ta shida, sai Teddyhits a waka ta daya zuwa ta hudu, sai kuma King D da Micky wadan da su ka tace wakokin tare da tabbatar da ingancin sautin.

Jarumin Lawan Ahmad ya samu karuwa ta haihuwa

Tin lokacin Musa Africa ya wallafa hoton artwork na wannan sabuwar kundin ne, mawakan da ya saka su a cikin wakar ke ta taya shi murna tare da daura hoton a suma na su shafukan na sada zumunci. Musa Africa wanda daya ne daga cikin manyan matasan mawaka da jahar Katsina kuma ya yi wakoki da dama da su ka sa aka san shi a duniyar mawakan Hausa Hip Hop.

Mawaki Salim Smart ya saki sabuwar waka

 

Leave your comment