Mawaki Shanawa ya na shirin sakin sabuwar bidiyo
6 April 2021
Picture source : Shanawa official instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararren mawakin Nanaye dan asalin garin Jos Ahmad Shanawa da ake wa lakabi da baban chakwai ya shirya sakin sabuwar fefen bidiyon sabuwar wakar sa mai taken "Soyayya Rayuwa", wacce ya saka matashir jaruma Ummisha a cikin ta.
Mawakin ya wallafa hoton shi da wannan jaruma ne a shafin sa na instagram tare da yi wa masoyan sa albishi da wannan sabuwar waka wacce ya ce za ta fito kwanan nan idan Allah ya yarda.
Jarumi Zango ya fito a cikin fim din "Gidan Badamasi" zango na uku
Ahmad shanawa wanda ya yi wakoki sanannu da ake sauraron su a wajajan nishadi daban daban a arewaci da ma wasu sassa na kasan nan, kwanakin baya ya samu karuwa ta haihuwa inda mawakin ya samu ya mace a cikin watan Maris da ta gabata na shekarar 2021.
Kamar yadda aka san mawaki Ahmad Shanawa da salon wakokin rausayawa dai, akwai alamun wannan sabuwar ita ma kamar sauran salon wakokin sa ne.
Leave your comment