Morel ya saki sabuwar bidiyon wakar sa
7 April 2021
Photo credit : Sals Fateetee instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Borno mazaunin babban birnin taraiyar Najeriya Abuja wato Morel ya saki sabuwar bidiyan wakar sa mai taken "Officer". A cikin farkon sabuwar watan Afrilun 2021.
Morel ya sanar da fitowar wannan sabuwar wakar ne a shafin sa na instagram mai mabiya mutun dubu dari biyu da doriya, tare da daura wasu bangaran bidiyon a shafin na sa. Wanda bidiyo da Morel ya saki shi ne bidiyan sa na farko a cikin sabuwar shekarar nan da mu ke ciki ta 2021.
Mawaki Shanawa ya na shirin sakin sabuwar bidiyo
Akwai tarin fitattun mawaka da jarumai har da ma su barkwanci a cikin wannan bidiyo na Morel da ya saki, cikin su akwai fitaccen dan barkwancin nan mai suna MC Tagwaye a matsayin Manager, akwai jarumi, mai shiryawa kuma mai gabatarwa a gidan talabijan wato Uzee Usman a matsayin Macho sai wadan da su ka yi fitowar musanman a cikin wakar irin su mawaki Khneegs, sai mawakiya Sals Fateetee, da ma'aikacin radio kuma mai editing din bidiyo tare da koyar da fadar kariya wato Spotlyt.
Morel wanda ya yi fitattun wakoki irin su "Aure", Hannu daya a sama" "Bullet" tare da M. I, "Antisocial" tare da Olamide, da sauran manya mawakan kudu irin su Reminisce, Phyno, sai irin su Ice Prince, da dai sauran su.
Ko a shekarun baya, Morel ya kasance daya daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop da su ka samu dama a kudu kafin dawowar sa Abuja da zama daga baya. Tini dai mawaka da dama su ka fara daura wannan bidiyo a shafukan su dan nuna ta su gudunmawar ga mawaki Morel.
Jarumi Zango ya fito a cikin fim din "Gidan Badamasi" zango na uku
Leave your comment