Mawaka sun yi wa Ado Gwanja bazata

Picture source : Ali Jita Instagram account 

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin salon nanaye kuma jarumin barkwanci a masana'antar Kannywood "Ado Isah" da aka fi sani da "Ado Gwanja" ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a ranar Talata shida ga watan Afrilu ta 2021.

Inda kuma abokan sana'ar sa mawaka manya su ka shirya ma sa bikin taya murna ta bazata a dakin cin abinci na babban hotel da ke Kano mai suna "Bristol palace". Tara da rare ma sa wakar birthday da aka fi sani a duniya, a lokacin da ake tsaka da fara cin abinci.

Da ba dan ni ba ne na yi, da na kai mawakin da ya yi wakar Ta na so kara kotu. "Mr Ladagoma".

Ado Gwanja cikin mamaki a fefen bidiyon da aka dauka ayayin gudanar da wannan bikin, ya yi mamaki da ya ga fitaccen mawaki Ali Jita ya kira sunan shi kuma ya ce wannan taron na taya shi murna bikin zagayowar ranar haihuwar sa ne. Kuma ragowar mawakan su ka kusanci inda Ado Gwanja ke zaune tare masa waka yayin da Nazifi Asnanic da Fresh Emir su ka cire ma sa hular sa, inda kuma Ali Jita da Umar M. Shareef su ka dinga wasa da gashin sa da ya tara irin na yan gayu mai cibircibir.

Acikin manyan mawakan da su ka halarci wannan bikin zagayowar ranar haihuwar Ado Gwanja sun hadar da:
Ali Isah Jita
Nazifi Asnanic
Husaini Danko
Adamu Nagudu
Umar M. Shareef
Jamilu Roja
Ahmad Shanawa
Sai matasan mawaka biyu suma da su ka halarci wannan taro da su hadar da:
Fresh Emir (Aku mai bakin magana), da kuma kallafi tsakanin ra'una wato Sals Fateetee.

Wannan kusan shi ne karo na farko da mawakan Arewa manya za su hada irin wannan bikin bazata dan taya wanin su murnar zagayowar ranar haihuwa, kuma muna fatan hakan zai cigaba domin zai kawo hadin kai da kuma cigaba mai daurewa a tafiyar su.

Jarumi Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau

Leave your comment