Da ba dan ni ba ne na yi, da na kai mawakin da ya yi wakar Ta na so kara kotu. "Mr Ladagoma".

Picture source : Mr Ladagoma instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop, marubuci kuma mai gabatarwa a gidajan radio a jahar Kano, wato Dabo Daprof wanda ake wa lakabi da Mr Ladagoma, ya baiyana cewa da ba shi ya yi wakar sa mai taken "Ta na so" ba, da tabbas sai ya kai karar mawakin kotu. Saboda yadda wakar ke saka shi a cikin yanayin zulumi da zurfin tunani a duk sanda ya saurare ta.

A cikin farkon makon nan ne na watan Afrilu ta 2021 ne mawakin ya baiyana hakan a shafin sa na Whatsapp, inda ya wallafa mabanbantan rubutu da ke nuna korafin sa akan wannan wakar ta sa da ya fitar cikin karshen watan December 2020 da ya gabata kuma ta samu karbuwa sosai tin fitowar ta.

Ko da masoyan Dabo Daprof su ka ga wannan rubutun, su ma wasun su sun baiyana suma halin da su ke tsintar kan su a duk lokacin da su ka ji wannan wakar mai taken "Ta na so". Har mu ka samu tattaro bayanan wasun su kamar haka:

Mutun na farko: Hakika dole ne wannan ta saka ko wani mutun zulumi, ya kuma sa masoyi tunawa da masoyiyar sa.

Mai rubutu na biyu: my star, kalaman ka su na sa ni zubar da hawaye a duk lokacin da na tuna da masoyi na da ya mun nisa.

Sai mai rubutu na uku ita ma ta ce: Ji nake kamar da ni kake a duk lokacin da na ji wakar, sai na ji kamar na rasa wani abu a rayuwa wani lokacin kuma ya sa ka ni nishadi.


Masoyan sa da dama ne su ka baiyana ra'ayin su akan wannan maganar da mawaki Dabo Daprof ya yi, kuma ya kara da cewa: bai taba nadamar yin ko wani waka ba kuma ita ma bai yi nadamar yin ta ba, amma tabbas ya na shiga zulumi da zurfin tunani akan "SO" idan ya ji wakar.

Jarumi Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau

Leave your comment