Ahmad Delta ya saki sabuwar waka da salon bazata.

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Kannywood kuma sabon Jarumi "Ahmad Delta" ya sake fitar da sabuwar waka kwanaki kadan bayan fitowar bidiyon wakar "Mafarki". Sai dai mawaki Ahmad ya shamashi masoyan sa a cikin wannan sabuwar wakar da ya sa wa suna da "Kina burge ni".

Mawaka sun yi wa Ado Gwanja bazata

Cikin satin nan ne na farko a watan Afrilu 2021 Ahmad Delta ya wallafa hoton wannan wakar a shafin sa na instagram, inda ya ke sanar wa mabiyan sa cewa ya saki sabuwar waka da sabuwar salon da ba akan sa aka san mawakin ba, Domin da salon gargajiya gargajiya yayi wakar sabanin irin salon da ya saba yi, kuma ya baiyana wa majiyar mu ta Madubi Naija cewa yayi hakan ne saboda ya gwada basirar sa a wani salon salon tare da kuma fadada masoyan sa wanda irin wannan salon da ya yi su su ka fi so.

Ahmad Delta, na daya daga cikin mawakan da su ke fitar da sabbin wakoki da bidiyo akai akai cikin sabuwar shekarar nan da mu ke ciki, kuma ana sa ran idan ya cigaba ahakan, zai iya zama daya daga mawakan da za'a yi yayin su a wannan shekarar ta 2021.

Jiya ya kare, Abdul D One ya saki sabuwar bidiyon sa.


Ahmad Delta kamar yadda da yawa su ka sani, haifeffen jahar Delta ne dake kudancin Najeriya kuma asalin iyayen sa daga kasar Nijar su ke. Daya ne kuma daga cikin yaran shahararren mawaki Husaini Danko.

Musan Danko ne makadin da ya yi aikin wannan sabuwar wakar ta "Kina burge ni", kuma tini masoyan mawakin su ka fara baiyana ra'ayin su akan wannan sabon salon da Ahmad Delta ya yi a cikin wakar.

An fara daukan wani sabon fim na Ali Nuhu.

Leave your comment