An fara daukan wani sabon fim na Ali Nuhu.

Picture source : Iinstagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A cikin wannan karshen makon data gabata ne na watan Maris 2021 aka fara daukan wani sabon fim mai taken "Burin Masoyi". Fim din da ya kara jarumai maza da mata ma su tarin basira da gwarewa a cikin sa, fim ne wanda Ali Nuhu ne ke da labarin, yayin da Sultan sheik isa alolo ya ke a matsayin mataimakin mai daukan nauyi, sai Lawan D. Funtua da kuma jaruma Hanan su ka dauki nauyin fim din.

Jiya ya kare, Abdul D One ya saki sabuwar bidiyon sa.

Wasu daga cikin jaruman da ke cikin wannan sabon fim sun hadar da:
Ali Nuhu
Halima Atete
Maryam Booth
Ramadan Booth
Hanan
Rukayya Dawaiya
Salisu Fulani
Amar Umar
Sayaya Sadiq
Da dai sauran su.

Wannan shirin fim dai an samu kwararrun ma'aikatan da ke daukan sa kuma jarumi Ali Nuhu a cikin hotunan da ya wallafa daga wajan daukan wannan fim, ya nuna alamun ba baiyana waye da waye mawakan cikin wannan fim ba.

Umar M. Shareef ya bude wuta a shekarar 2021

Ali Nuhu wanda a kwanakin baya ne ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa ya na cigaba da rike kambun sa na sarkin Kannywood, musanman idan aka duba irin finafinan da jarumin ya ke fitar wa da kuma wadan da ake saka shi a cikin su yadda su ke karbuwa a gurin ma su kallon finafinan Hausa na Kannywood.

Mawaka sun yi wa Ado Gwanja bazata

Leave your comment