Jiya ya kare, Abdul D One ya saki sabuwar bidiyon sa.

Picture source : instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawaki kuma jarumi mai tasowa a masana'antar Kannywood Abdul D One ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Ko za'a fasa" a cikin farkon watan Afrilu na 2021.

Mawaka sun yi wa Ado Gwanja bazata

Wakar da ka yi ta a bakin taku da ke jahar Legas da ke kudancin kasan nan, ya fito da wani sabon salon yadda bidiyon wakokin Nanaye aka san su da shi, kuma an masa aikin da ya yi daidai da wakar. Abdul D One ya sanar da fitowar wannan wakar ne a shafin sa na instagram kuma ya sanar da masoyan sa da cewa za su iya zuwa su sauke wannan wakar daga shafin sa na YouTube.

Umar M. Shareef ya bude wuta a shekarar 2021

Mawakin wanda ke karkashin shahararren mawaki Umar M. Shareef ya sanu ne tin bayan da kwamfanin shirya finafinai ta jarumi Ali Nuhu, wato "FKD" ta saka wakar sa a cikin fim din "Mansoor" mai taken "Abun da ke raina", da su ka yi tare da mawakiya "Khairat Abdul" yar asalin Kaduna

Mustapha M. Shareef ne ya yi aikin bidiyon, ayayin da jaruma Aisher Aliyu ta fito a matsayin budurwar sa a cikin wakar. Mawaka da dama ne su ke ta wallafa wannan bidiyon a shafukan su tare da taya mawaki Abdul D One fatan alheri.

Jarumi Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau

Leave your comment