An fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a salon waka.

Picture source : S Bono instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A cikin wannan karshen makon data gabata ne na watan Maris 2021 aka fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a karkashin kwamfanin Umar M. Shareef mai taken "Soyayya Ce". Fim din da ya tara jarumai maza da mata ma su tarin basira da kwarewa a cikin sa musanman kananan jarumai da kuma sabbin fuskoki.

Ahmad Delta ya saki sabuwar waka da salon bazata.

fim ne wanda Nazeer H Maiatamfa ya rubuta labarin da baitin, kuma ya dauki nauyin aikin, yayin da Aminu S. Bono ya bada umarni. Sai Usha Vocal a matsayin mai kwalliya, Nazifi kala a matsayin mai hotu da daukan fim din. Smalljezzy ya samar da tufafi sai matasan kannywood su ka samar da inda za'a dauki fim din.


Wasu daga cikin jaruman da ke cikin wannan sabon fim sun hadar da:
Aminu S. Bono
Kb international
Leemer Queen Dz
K gamal Aboki
Da kuma Nazeer H. Maiatamfa Da dai sauran su.

An fara daukan wani sabon fim na Ali Nuhu.

Duk da dai babu wani sanannan furka a cikin wannan sabon fim a manyan jarumai, amma ana ganin zai samu karbuwa saboda shirin na dogon zango ne kuma yawancin irin wadan nan finafinai ne ke samun karbuwa a wajan yan kalo a halin yanzu. Irin su Izzar so, A Duniya, Kaddarar so da dai sauran su.

Umar M. Shareef ya bude wuta a shekarar 2021

Leave your comment