Tashar musulinci za ta fara haska finafinan Kannywood

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Babbar tashar musulinci na talabijan mai suna African TV3 zai fara haska wani sabon fim daga jaruman masana'antar Kannywood mai taken "Iyalina" a cikin mako na biyu a watan Afrilu 2021.

Fresh Emir ya saki sabuwar waka

Wannan fim mai dogon zango da za'a fara haskawa, na nuna labarin rayuwar iyaye da yayan su da kuma irin fama da su ke dan tarbiyan tar da su kafin su gaji aiki ko sana'ar su idan sun tsufa. Kuma wannan gidan talabijan ta Africa TV3 da zai ke haska wannan fim, su suka dauki nauyin shirya wannan fim na "Iyalina".

Babban mai bada umarni a Kannywood Aminu S. Bono ne ya bada umarnin wannan fim, kuma an sanya manyan jarumai da ma kananan a wannan fim dan kayatar da ma su kallo tare da isar da sakon da ya dace a cikin ta.

Abun da yake kara jan hankalin mabiya finafinan Kannywood shine ganin tashar musulinci ce ta dauki nauyin wannan fim, kuma za ta dinga haskawa a ko wacce sati, domin ana ganin kamar malaman addini da dama su na chacchakar jaruman akan yadda finafinan su ke taba barbiya da kuma rinjayar dabiyar ma su kallon su.

An fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a salon waka.

Ahmad Delta ya saki sabuwar waka da salon bazata.

Leave your comment