Fresh Emir ya saki sabuwar waka

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Matashin mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kano Fresh Emir (Aku mai bakin magana) ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Yaya ne?" a jiya ranar juma'a 9 ga watan Afrilu 2021 da mu ke ciki a manyan shafuka da manhajojin sauke waka a zamanance.

Tin a ranar Alhamis 8 ga watan Afrilu 2021 ne, mawakin ya yi wannan sanarwar ta sakin sabuwar wakar a shafin sa na instagram, yan kwanaki kadan bayan fitar wakar Salim Smart da Fresh Emir din ya fito a cikin wakar mai taken "Mai kike nufi".

Mahaifin Abdul Zero ya rasu.

Wannan waka dai makadi Mega Mix daga jahar Kano ne ya yi aikin wakar, kuma tini masoyan sa da dama da su ka saurari wannan wakar su ka fara baiyana ra'ayin su akan wannan sabuwar wakar ta Fresh Emir.


A cikin lokaci kalilan hankali ya karkata akan salon wakokin da Fresh Emir ya ke yi akan Al'umma da halin zamantakewa da kuma gwamnati. Ya kuma samu wannan nasarori ne a bisa gudunmawa da ya ke samu daga wadan da su ke da ruwa da tsaki a tafiyar sa irin su Mus'ab Dauda Sadauki wanda shine manajan Fresh Emir, kuma daractan sa da kuma mai masa promo da fitaccen kafafen nan biyu mallakin su ma su suna Haudatop ta yanar gizogizo da kuma tashar su ta Hausatop TV na YouTube.

Mawakiya Khairat ta fitar da bidiyon ta da Hamisu Breaker

 

Hakazalika shima fitaccen mawaki Dabo Daprof Mr Ladagoma jagora ne a tafiyar Fresh Emir, musanman a fanin fassara wakokin "A yau series " da kuma "Wasika ga shugaban kasa", sannan da sauran harkokin rubucerubuce da shawarwari a tafiyar. Sai mai bada umarni Msk shima jigo ne a tafiyar Fresh Emir a fanin dauka da editing bidiyon sa a matsayin mai tallafa wa Mus'ab da kuma bada shawarwari shima.

Sai yayan Mus'ab wato Anas Sadauki wanda ya ke tallafa wa da kayan aiki da kuma fannin gudunmawa ta kudi dan gudanarwa. Akwai abokin su mai jan mota idan Zach su fita aiki ko taro wato Kwankwamai mai gidan TV kamar yadda su ke masa lakabi.

An fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a salon waka.

Muna fatan mawaki Fresh Emir zai cigaba da sakin wakoki akai akai kamar yadda aka san shi akan wannan salon.

Jiya ya kare, Abdul D One ya saki sabuwar bidiyon sa.

Leave your comment