Mahaifin Abdul Zero ya rasu.

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin fitattun matasan mawaka kuma makadi a masana'antar Kannywood Abdul Zero dan asalin jahar Gombe, a jiya ne Allah ya yi wa mahaifin shi rasuwa bayan yar gajeriyar rashin lafiya da ya gamu da shi a lokacin da ya je ta'aziya jahar bauchi na rasuwar da aka ma sa achan.

Mawakiya Khairat ta fitar da bidiyon ta da Hamisu Breaker

A jiya juma'a ne Allah ya yi wa mahaifin mawakin rasuwa a jahar Bauchi. Kuma tini a ka yi jana'izar sa a bisa tsarin addinin musulunci. Inda tin a jiyan ne Abdul Zero ya baro garin Kano dan halattar jana'izar mahaifin sa.

An fara daukan wani sabon fim na Ali Nuhu.

Mawaka da dama ne da kuma jarumai su ka taya Abdul Zero jajen wannan rashi da ya yi, tare da taya shi da adduar jure rashin. Abdul Zero na daga cikin manyan yaran jarumi kuma mawaki Adam A. Zango ne tun a shekarun baya, kuma ya yi wakoki da dama da kuma kidekide ma su yawa ga manyan mawaka ciki har da Adam Zango din da kuma Ado Gwanja.

Muna mika sakon ta'aziyar mu ga Abdul Zero akan wannan rashin da ya yi da fatan samun dangana tare rokawa mahaifin rahama amin.

An fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a salon waka.

Leave your comment