Rahama Sadau da Ali Jita sun nishadantar da mutane a Kano

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararreyar jarumar Kannywood da Nollywood yar asalin jahar Kaduna Rahama Sadau da fitaccen mawakin Hausa a salon Nanaye Ali Jita sun halacci taron kaddamar da sabbin nauyikan Maltina da aka samar guda biyu.

Wadan nan sabbin nauyikan su ne Maltina nauyin Vanilla da kuma nauyin pineapple. Wadan nan kari ne akan sananan nauyin Maltina Classic da kowa ya sani.

Salim smart da Khairat sun sake yau sabuwar waka tare.

Taron kaddamarwar ya gudana ne a katafaren wajan ajiye motoci a cikin kasuwar zamani ta Ado Bayero Mall da ke jahar Kano, a yau Lahadi 11 ga watan Afrilu 2021 tin daga karfe 11 na safe.

An yi wasanni daban daban a wajan wannan kaddanarwar da su kuma tarin jama'a da su ka samu halatar wannan waje, maza da mata har da kananan yara da kuma yan makaranta.

An fara daukan wani sabon fim mai dogon zango a salon waka.

Masu gabatarwa biyu ne su ka jagoranci gabatarwa a wajan da su ka haka da MC Musa da MC Omo Oba, sai kuma ma su sarrafa sauti mutun biyu su ma da su ka hakar da Dj Tiny da kuma Dj Dee wanda shi ne Dj din fitaccen mawaki Ado Gwanja.

Rahama sadau wacce jakadiyar kwamfanin Martina ne ta kasance a kan gaba wajan samun irin wadan nan damammakin na zama jakadar manyan kwamfan a Najeriya.

Tashar musulinci za ta fara haska finafinan Kannywood

Leave your comment