Kamilu koko ya hana ni kudin da Rarara ya bashi ya bani -AleeGee

Picture source : AleeGee and Kamilu instagram accounts

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop kuma makadin zamani dan asalin jahar Katsina mazaunin jahar Kano "AleeGee" ya koka da mawakin siyasa "Kamilu koko", akan ya cinye kudin da Rarara ya bashi ya baiwa shi mawaki AleeGeen.


A cewar shi AleeGee, shekara guda kenan da shahararren mawakin siyasa a nahiyar Africa "Dauda Kahutu Rarara" ya baiwa Kamilu Koko naira dubu talatin ya baiwa AleeGee, dan ya rage radadin zaman gida a lokacin lock down da aka saka sakamakon bulluwar annobar Corona Virus.

Amma abun mamaki a cewar AleeGee, har shekara daya ta zagayo da faruwar wannan abu, amma har yanzu naira daya Kamilu koko bai bashi a cikin wannan dubu talatin da Rarara ya bayar ya bashi ba. Kuma yasan da cewa shi AleeGee yasan da zancen kudin.

Rahama Sadau ta yi rabon kayan abinci ga mabukata

Wannan dalilin ne ya fusata mawaki AleeGee har ya daura hoton mawaki kamilu koko a shafin sa na instagram, tare da kiran sunan sa kai tsaye, kuma ya tinatar da shi maganar kudin. Harma ya kara da cewa "idan bai biya shi anan duniya ba, zai biya shi a kiyama".

Gidan Danger kashi na bakwai ya fito

Wannan kusan shi ne karo na farko da wani mawaki ko jarumin fim a arewacin Najeriya zai dauki irin wannan matakin akan wanda ya cinye mai hakkin sa ko ya cuce shi akan kudi ko wani abu makamancin hakan.

Sai dai wani abun dubawan anan shine yadda wannan mawakin siyasa da AleeGee ya zarga da cinye mai kudi ya ke da rufin asiri daidai gwargwado kuma ba matashi bane akwai shekaru akan sa, amma kuma sai ga wanda bai kai shi samu ba kuma a shekaru kasa yake da shi ya fito yana tozarta shi a idon duniya sakamakon hakkin sa da ya ci.

Har yanzu Rarara bai ce komai akan wannan maganar ba, amma masoyan AleeGee da dama sun yi Allah wadai da abun da Kamilu ya yi wa AleeGee.

Ahmad Shanawa ya Saki Sabuwar Bidiyo

Leave your comment