Rahama Sadau ta yi rabon kayan abinci ga mabukata

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararriyar jarumar fim a masana'antar Kannywood da Nollywood yar jahar Kaduna wato "Rahama Sadau" ta bude sabon watan Ramadan ne da rabon kayan abinci ga mabukata da dama a yau daya ga watan Ramadan ta shekarar 1442, wacce ta yi daidai da 13 ga watan Afrilu 2021. A jahar ta na haihuwa wato Kaduna.

Gidan Danger kashi na bakwai ya fito

Yau da rana ne jarumar ta gudanar da wannan rabo a karkashin kungiyar nan mai suna "Ray of hope", tare da taimakon wasu daga makusantan ta wajan gudanar da wannan abun alheri.

Tin abaya, daman jarumar na daya daga cikin jarumai ma su tallafawa mara sa karfi da marayu a karkashin kungiyoyin sa kai da tallafi da su ke da su. Jarumai irin su Saratu Gidado da matar Sani Danja Mansura Isah, na kan gaba a jarumai ma su irin wannan tallafin daga Kannywood.

Ahmad Shanawa ya Saki Sabuwar Bidiyo

Magoya bayan jarumar da dama ne su ka yabawa kokarin ta a shafukan sada zumunci daban daban tare da kira ga sauran jarumai da su yi koyi da irin wadan nan aiyukan alheri da Rahama Sadau ke gudanarwa a cikin Al'umma.

Leave your comment