Maryam Booth za ta sake fitowa a wani sabon fim na yan kudu.

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar yar wasan Hausa a masana'antar fim ta Kannywood da kuma jaruma a Nollywood wato Maryam Booth yar asalin jahar Kano za ta sake fitowa a wani sabon fim mai taken "Under Belly" a kwanan nan.

Wannan sabon fim da jarumar ta fito a ciki, ya hada da wasu kwararru kuma sanannun jarumai irin su Ali Nuhu shima daga Kannywood, Femi Adebayo Salami, Stannze da Kunle Coker da dai sauran su. Kuma za a haska wannan fim ne a gidajan haska finafinai daban daban a kasar nan idan lokacin sakin sa ya yi.


Maryam Booth wacce ta fito a cikin wani fitaccen fim mai taken "Sons of the caliphate" ta taka rawa a wannan sabon fim din kuma a cewar ta, wannan fim a wajan mu ratio ne kuma muna alfahari da shi.

Mawaki 442 ya yi kira ga masu shiga tsakanin bawa da ubangijin sa.

Kawo iyanzu ba su baiyana ranar da wannan fim zai fito ba, sai dai duba da yanayi na azumi, ta yo zuwa bayan sallah karama wannan fim mai suna "Under Belly" ya fito. Masoyan jarumar a shafin ta na instagram da dama ne su ka tofa albarkacin bakin su akan wannan batu da jarumar ta wallafa.

Mansura Isah bana ta yi rabon abinci kamar yadda ta saba

Leave your comment