Jaruma Hafsat Idris ta Siyi Sabon Mota.

[Photo cred: Instagram - Hafsat Idris]

by Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararriyar jarumar fim na masana'antar shirya finafinai ta Kannywood Hafsat Idris ta yi saya wa kan ta tsayeyen sabuwar mota kirar "Marsandi 4matic GLA 250" a cikin watan azumi na Ramadan.


Jarumar ta sanar da hakan ne yau 22 ga watan afrilu 2021, a shafin ta na instagram da facebook. Kuma ta taya kan ta murnar siyan wannan sabuwar motar a kasan hotunan motar da ta daura.

Also Read: Fresh Emir ya saki sabuwar bidiyo.

A daidai lokacin da jarumai da mawaka da kuma ma su bada umarni ke rabon motoci ga makusantan su a yan kwanakin nan, ita kuwa Hafsat Idris siya wa kan ta tayi, wanda hakan ya jawo hankalin mabiyan ta a shafukan sadarwa na zamani, inda wasun su su ka ce akwai ayar tambaya akan yadda jarumai mata ke samun kudi a masana'antar fiye da yan uwan su jarumai maza.


Ko a farkon watan nan jarumar ta yi rabon abinci ga mabiyan ta da kuma mabukata dan raje mu su radadin halin da ake ciki a watan azumin bana.


Idan aka yi duba da yanayin da al'umma su ke ciki a kasar nan, za a ga cewa talaka na cikin mawuyacin halin da ya ke neman dauki da tallafi dan samun sauki. Hakan ya sa Jarumar ta chanchanci yabon mutane da dama domin tallafin ya zo ne a daidai lokacin da ake bukatar ta.

Leave your comment