Fresh Emir ya saki sabuwar bidiyo.

Picture source :Iinstagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa Hip Hop Adam Abdullahi dan asalin jahar Kano da duniya ta fi sani da "Fresh Emir " ya saki sabuwar waka tare da bidiyon ta a yau talata 20 ga watan afrilu 2020.

Mawakin ya sanar da fitowar wannan sabuwar waka da bidiyon ta a shafin sa na instagram, awanni kadan kafin sakin ta a yanar gizo. Kuma ya saki wannan wakar ne a daran yau bayan bude baki na azumin watan Ramadan.

Wannan wakar mai taken "Jita jita", waka ce da wata gidauniya mai zaman kan ta ta dauki nauyin wakar, a cikin yunkurin ta na yaki da masu yada labarin karya da kuma jitajita musanman ta kafofin sadarwa na zamani mabanbanta da ake yada labarai da su.

Mawakan Hausa Hip Hop da watan Ramadan
Tin a cikin shekarar da ta gabata ne wannan kungiya ta kirkiri wannan kamfen a jahar legas, inda ta gaiyaci masu basira da kuma mabiya a wadan nan kafafe na zamani, dan tattauna mafita akan mai ya dace ayi wajan wayar da mutane illar yada irin wadan nan labarai, wanda Fresh Emir na daya daga cikin mawakan da su ka halarci wannan kamfen a legas kuma daga nan ne wannan waka ta samo asali.

An dauki bidiyon wakar a jahar Kano, inda mai bada umarni MSK ya yi aikin tare da taimakon shima mai bada umarni Mus'ab Dauda Sadauki da aka fi sani da Director Mus'ab. Fitaccen Mawaki kuma Marubuci Dabo Daprof ya fassara wakar zuwa harshen Turanci, yayin da makadi Mega mix ya yi aikin audio din wakar.

Maryam Booth za ta sake fitowa a wani sabon fim na yan kudu.

Tini sama da mutane dubu biyar da doriya su ka kallin wannan fefen bidiyo a shafin mawaki Fresh Emir na instagram daga lokacin da ta fito, kuma wannan shi ne aiki na farko da mawakin ya fitar nasa na kan sa tin bayan wakar Wasika ga Shugaban kasa ta biyu da ya yi.

Leave your comment