Mawakan Hausa Hip Hop da watan Ramadan

Picture source :Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Manyan mawakan Hausa Hip Hop daga jahohi daban daban a kasar Najeriya ne su ke fuskantar wannan watar ta Ibada na Ramadan. Kuma hakan ya sa wasu da dama daga cikin su ajiye duk wani sha'ani daya shafi waka.

Yayin da kuma wasu daga cikin su ke mayar da shafukan su wajan fadakar da yan uwa da kuma jan hankalin su ga maida lamarin su ga ubangiji dan neman gafara da kuma ibada.


Mawaka irin su Mr 442 su na wa mabiyan su Labarin haihuwar manzan Allah S.W.A da kuma kira ga mutane akan su bi Allah yadda ya dace.

Shi kuwa mawaki kuma marubuci Dabo Daprof ya kasance a ko wace wana rubutu yake gajeru dan kira ga mutane akan darasi na rayuwa, wanda ya fara tun a ranar farko na watan Ramadan.


Ita ma mawakiya kuma yar jarida Queen Zeeshaq, a shafin ta na facebook kiraye kiraye ta ke ga mutane da su dage wajan ibada da kuma taimakawa ma ra sa Karfi a cikin wannan watan.

Su ma ragowar mawakan su na cigaba da kira ga mutane game da falalar wannan wata mai albarka ta shafukan su na sada zumunci.

Leave your comment