An Kwace wa Mawakiya Queen Zeeshaq Instagram Account

[Photo cred : Queen Zeeshaq's Facebook]

by Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram


Fitacciyar matashiyar mawakiya a masana'antar Hausa Hip Hop yar asalin jahar Kano kuma yar jarida Zainab Ishaq wacce aka fi sani da suna Queen Zeeshaq ta rasa instagram account din ta a cikin makon nan da mu ke ciki.

Also Read: Mawakan Hausa Hip Hop da watan Ramadan


Mawakiyar wacce ke gabatar da shirin Hausa Hip Hop a daya daga cikin gidajan radio da ke garin Kano, wacce aka wa shirin suna "Hausa Hip Hop Square", ta sheda wa majiyar mu faruwar wannan alamari ta shafin ta na facebook, awanni bayan da ta gano cewa wani ko wasu da ba a san waye ba ya kwace wa mawakiyar instagram account din ta kuma har ya fara kokarin danfarar mabiyan ta ta hanyar jawo hankalin su kan saka hannun jari a wani harkar hadahada ta yanar gizo dan samun riba da yawa.


Mawakiyar ta sanarwa mabiyan ta a shafin ta na facebook cewa an kwace mata account kuma ba ita ba ce ke neman taimako daga wajan su ko tallata mu su wannan harkar da ake talla da shafin na ta na instagram.


Wannan kwacewa Queen Zeeshaq instagram account ya biyo bayan da shima jarumin Kannywood Adam A. Zango ya rasa shima tasa instagram account din ne, duk da kuwa ya na da mabiya sama da miliyan daya da yan kai. Daya daga cikin mawakan da su ka taya mawakiyar yada labarin kwace ma ta account da aka yi shine fitaccen mawaki, marubuci kuma aminin mawakiyar mai suna Dabo Daprof.


Sai dai mu ce muna taya mawakiya Queen Zeeshaq alhinin wannan rashi da kuma fatan mabiyan ta za su kula dan gudun fadawa a hannu wadan nan bata gari.

Leave your comment