Mansura Isah Ta Koya Wa Nakasassu 50 Aikin Hannu
29 April 2021
Picture source : Mansura Isah instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararriyar jaruma Mansura Isah kuma daya daga cikin fitattun matan Arewa ma su taimakawa mara sa karfi ta karkashin gidauniyar su, wacce ta yi fice a rabon abincin, magunguna da sauran kayan bukata ga mabukata kamar yadda ta saba duk watan Ramadan da ma sauran watanni, ta koya wa nakasassu (masu bukata ta musanman) aikin hannu har mutane hamsin(50), a karon farko.
Jarumar ta yi wannan rabon ne a karkashin gidauniyar ta mai suna "Today's life foundation", inda ta sheda wa mabiyan ta a shafin ta na instagram cewa, sun yi nasaran koyar da masu bukata ta musanman mutun 50 aikin hannu a cikin mutane 100 da gidauniyar ta kudiri aniyar koya wa aikin hannu dan dogaro da kai da kuma barin kan titinu inda yawancin su ke barace barace.
Jarumar ta nuna farin cikin ta tare da kwalla ta murna a lokacin da daya daga cikin wadan da su ka amfana da wannan tallafi ya gabatar ma ta da jakar da ya hada tare da baiyaba mata cewa ya hada wa yar sa kuma bayan ya bata yar ta yi farin ciki tare da tambayan sa a ina ya siya. Ko da ya ce ma ta shi ya hada da hannun sa, yar bata yarda ba.
Mansura Isah ta ce mutane hamsin na farko an koya mu su yadda ake hada jakankunan hannu da takalma, ragowan mutane hamsin kuma za a koya mu su yadda ake sabulu, Omo, Hypo, kayan kamshi da dai sauran su.
Jarumar wacce ta ke samun tallafi daga wasu daidaikun mutane ma su taimakawa da kayan abincin kudade da kuma sauran kayan tallafi.
Leave your comment