Ji na ke makar na kashe kai na a halin yanzu - Jaruma Ummizeezee

Picture source zeezee instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood kuma tsohuwar mawakiyar R and B Ummizeezee ta fito ta baiyana cewa ta na so ta kashe kan ta saboda halin damuwa da kunci da jarumar ke ciki a halin yanzu.


Jarumar ta yi wannan sanarwar ne a shafin ta na instagram bayan da ta daura wani hoton ta da ya nuna fuskar ta da damuwa, wanda kuma a cikin harshen turanci ta taiyana halin da ta ke ciki da kuma abun da zuciyar ta ke raya mata ta yi.

A cikin kalaman ta, jarumar ta ce: a halin yanzu ina rayuwa takaici da har ina jin na kashe kai na kawai, amma ba na so kowa ya tambaye ni mai ke damu na, kawai abun da na ke bukata daga wajan ku addua.


Wannan rubutu ya samu martani sama da dubu daya da dari biyu daga mabiyan jarumar da ma wasu jaruman da ke bin ta a shafin ta na instagram. Kuma wa su daga cikin wadan da su ka yi mata magana akan wannan hukunci da zuciyar ta ke raya mata sun hadar da jaruma Maryam Booth da kuma yar uwar ta na jini Hasina yar chana.

Har yanzu babu wanda ya san dalilin wannan halin da tsuhuwar jarumar ke ciki, amma daga dukkan alamu wannan maganar da Ummizeezee ta yi ya dauki hankalin mutane da dama kuma suna ganin ta na bukatar taimakon gaggawa daga makusantan ta gudun kada ta aikata abun da zuciyar ta ke raya mata.

Jarumi Umar Gombe ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau

Morel ya saki sabuwar bidiyon wakar sa

Mawaki Shanawa ya na shirin sakin sabuwar bidiyo

 

Leave your comment