Matasa: Mawakan Zamani da Mawaka Masu bin Salon Gargajiya
22 March 2021
[Image Source: Instagram]
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Yayin da duniya musamman a nan Afirka ke samun sabon salon kida wanda ake cewa Afrobeats, a nan kasar Hausa mawaka irinsu Adam Zano, Umar m Shariff, Hamisu Breaker da dai sauransu, sun zabi su bi zamani ta hanyar kalamansu, salon wakokinsu da dai yanayin yadda suke tsaran wakokin.
Mawaki Umar MB ya fitar da sabuwar kundin waka
A gefe daya kuma, mawaka irinsu Aminu Alan Waka, Nasiru Sakin Waka su kuma sun zabi su rike irin nasu salon wanda ya fi kama da na gargajiya. Za ka iya gane haka ta hanyar kalamansu da kuma irin kamun kai musamman daga wajen Aminu Alan Waka.
Tambayar anan ita ce, su wane ne a yanzu suke jan ragamar?
Wasu ka iya cewa mawakan zamani. Wasu su ce salon gargajiya ya fi. To Hausawa dai na cewa ba a san maci tuwa ba sai miya ta kare.
Mawaki Deezell ya fitar da sabuwar waka
Babban abin da ake so a waka shi ne nisahdi da kuma isar da sako mai ma’ana ta hanyar ilimantar da al’umma da kuma nunarshe su abin da mutum ya hango ta hikima da basira.
Ku a naku ra’ayin, su wane ne ja-gaba?
Hausa Music Hanny Billy-O, Freeboi Shaban: Yaran mawaka yan na gada.
Sayyada Rabi'abu S. Haruna Music: An yi babban rashi a duniyar mawakan yabo.
Leave your comment