Download Hausa Music: Billy-O ya na shirya fitar da wata wakar hadaka.

picture source: Billy-O Instagram page

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawaki kuma Jigo a masana'antar Hausa Hip Hop Alhaji Bello Ibrahim da aka fi sani da Billy-O ya shirya fitar da wata sabuwar wakar hada ka da ya sanya wa suna "Arewa23" a cikin wannan shekarar da mu ke ciki ta 2021.

Mawaki Umar MB ya fitar da sabuwar kundin waka

Mawaki Billy-O ya baiyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta bakin makusancin sa wato mawaki Dabo Daprof a yau alhamis 18 ga watan Maris.

Mawaki Deezell ya fitar da sabuwar waka

Wannan wakar za ta kasance irin ta na farko a tarihin masana'antar mai dauke da mawaka da su ka kai wannan addadin a cikin waka guda, duk da dai mawaki Billy-O bai baiyana dalilin sa na hada irin wannan wakar ba, amma daga dukkan alamu waka ce da watakila akan kasa ko matsalolin al'umma za'a yi akai. Kamar yadda yawancin wakokin hadaka su ke kasancewa.


Tin bayan fitowar fefen bidiyan wakar Billy-O ta "Ina son ki" ne mawaki Billy-O ya fara shiryeshiryen fitar da wani sabon aikin kamar yadda majiyan mu ya sheda mana.

Sai dai babu wanda ya kawo cewa tsohon mawakin na shirin fitar da irin wannan wakar ta hada ka ba, kuma wani abun jan hankalin anan shi ne wadan nan mawaka Billy-O zai saka a cikin wannan wakar ta hadaka, duba da alakar sa da daruruwan mawaka manya da kanana a masana'antar Hausa Hip Hop.

Muna dakon fitowar wannan aikin kuma da zaran ta fito, za mu sanar da ku anan Mdundo.

Hausa Music Hanny Billy-O, Freeboi Shaban: Yaran mawaka yan na gada.

Sayyada Rabi'abu S. Haruna Music: An yi babban rashi a duniyar mawakan yabo.

Leave your comment