Darasin da mawaka masu tasowa zasu bi domin su shahara kaman gwanayen su

By El-Yaqub I.I

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Ba shaka kasar Najeriya itace jagaba idan aka zo fannin yawan mawaka ba ma a Afirka kadai ba, atta duk duniya.

Duba da tarin yawan mawakan da kasar ta Najeriya Allah ya albarkace ta da shi musamman a salo daban-daban, akwai mawaka wadanda suke kokartawa domin su shiga masana'antar. Wannan me yasa aka kasapta mawaka gida biyu wato gwanaye da kuma masu tasowa. Gwanaye sune wadanda suka jima a cikin harkar shekara da shekaru sannan masu tasowa sune sabon shiga cikin masana'antar wadanda basu waye cikin harkar waka ba.

Fitattun dandalin sada zumunci guda 6 domin tallata hajjar mawaki

Ga mawaka masu tasowa da sabon shiga, suna da darasin da ya kamata su koya kamun a ce sun zama gwanaye saboda akwai mawaka da dama wadanda suka yi shura a duniyar ta waka. Ga wasu darusan da zai taimaka wa mawaka masu tasowa domin suma su zamto gwanaye wanda za ayi koyi da su. 

1. Daidaituwa
Akwai matukar wuya wurin tara dumbin masoya da waka daya tak. Domin samun nasara a fagen waka, ya kamata shi mawaki ya samu daidatuwa wajen sakin wakoki a kai a kai sannan wakokin su zama madu inganci. 

Mawaka wadanda suka yi shura a Najeriya yau sun samu nasarar hakan ne saboda nuna daidaituwa da jajircewa wurin sakin wakoki masu inganci da nishadantarwa. Wannan ne ya basu daman samun tarin masoya wanda ya kan janyo su su saurari wakokin su a kan yanar gizo ko su saukar da su domin saurarar su sannan su kan bafa gudumawa wajen rarraba wakoki mawakan ga yan uwa da abokan arziki. 

2. Ingantacen aiki 

Abu daya ne ka saki waka, ko gajeren kundi (wato EP) ko cikaken kundi (wato LP) sannan abu daya ne ka saki wakoki masu inganci. Waka ko kundi mai inganci daga ji an sani ba sai ka yi dagiya a kai ba saboda duk wakar da take da inganci tana tallata kan ta da kan ta. Wakar da ta hadu ta kan janyo masoya su nemi wakar domin su saurara ko su kalla sannan wannan yana nufin cewa shi mawakin zai cigaba da samun sabbin masoya idan har ya cigaba da fitar da ayuka masu inganci. 

Inganci yana nufin aikin da aka saman ma sa kida mai dadi, baiti da kari mai dadi, an tace aikin da kyau sannan ayi wa aikin tacewar karshe wato "mastering" domin sautin ta dauki hankalin masu sauraro. 

3. Hadin gwiwa

Akwai mawaka da dama wadanda suka yi fice saboda hadin gwiwa da wasu mawakan. Ga duk wani mawaki mai tasowa, zasu iya aiki da mawaki akalla daya zuwa biyu domin a san da zaman su. Wannan zai taimaka matuka wajen kara daga likkafan shi mawakin mai tasowa. 

Hanyoyi 6 da wakokin ka zasu shahara a dandalin TikTok

4. Kwarewa wajen amfani da dandalin sada zumunci

Dandalin sada zumunci yanzu ya zama tamkar babban dukiya ga duk wani mawaki wanda yake neman ya shahara a masana'antar. 

Gwanayen mawaka sun saba suna hada allaka da masoyan su ta bangaren sauraron su, nishadantarwa ta hanyar amsa tambayoyin su sannan ta wannan hanyar ne su kan san abun da masoyan su suke bukata daga wajen su. 

Kulla alaka/zumunci tsakanin mawaki da masoyan sa, yaďa tsofofi da sabbin wakoki hanyoyi ne wanda mawaka zasu isar da sako ga masoyan su a kai a kai idan har suna so su zama gwanaye domin duniya ta san da su.

Leave your comment