Fitattun dandalin sada zumunci guda 6 domin tallata hajjar mawaki
13 September 2021
[Photo credit: El-Yaqub I.I ]
by El-Yaqub Isma'il Ibrahim
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Dandalin sada zumunci ya zamto tamkar iskar da ake shaka a rayuwar dan Adam a wannan karnin. Ko ta hanyar sada zumunci da yan uwa da abokan arziki, ko ta hanyar zamantakewa da abokan hulda ta hanyar yanar gizo, dandalin sada zumunci ya zama gishirin miya a rayuwar da muke ciki yanzu.
6 Proven Ways To Make Your Music Go Viral on TikTok
Bayan amfanu dake tattare da dandalin sada zumunci, al'umma da wuraren kasuwanci sun yi matukar kokari wurin amfani da dandalin domin tallata hajarsu domin su samu kudi ko su kara bunkasa sana'ar su.
Mawaka kamun wannan karnin su kan fuskanci kalubale wurin tallata wakokin su amma da zuwan dandalin sada zumunci, ya kara buda wasu hanyoyin. Tambayar yanzu itace wace dandalin sada zumunci ya kamata mawaki ya kamata ya yi amfani da shi wurin tallata wakokin sa. Wannan rubutaciyar kasidar zata matukar baka gudumawa idan ka karanta cikin natsuwa.
1. Facebook
Bullowar sabbin kafafan dandalin sada zumunci a duniyar yanar gizo sam bai kawo tasgaro ga shafin na Facebook ba. Wannan dandalin dai na da masu amfani kimanin biliyan 2.89 duk wata wanda ya saka shafin a mazaunin dandalin da tafi shahara a duk duniya.
Da Facebook, za ka iya raba wakokin ka hade da tallata ta ga abokai, ko kuwa ga wadanda kake so su gani ta shafin rukuni da bangaren tallace-tallace ta Fcebook da ma sauran su. Facebook na tattare da duk abun da kake bukata. Yana kunshe ne da abubuwan da sauran shafukan sada zumunci suke da shi.
Yana bada daman raba link na wakokin ka kai tsaye ga abokai ko masoyan ka sannan masoyanka zasu iya samun wakar ka idan suka latsa link din kai tsaye. Dandalin na Facebook zai baka daman haska bidiyoyin ka ga masoyan ka ko kuwa za ka iya hawan Facebook live domin masoyan ka su tattauna da kai kai tsaye.
2. Telegram
Telegram wani dandali ne wanda aka kirkire shi ne a shekarar 2013 mai yawan masu amfani da shi kimanin mutane miliyan 500. Shafin na Telegram yana da wani sashi mai sunan "channels" wanda mawaka da madu talla zasu iya amfani dashi wurin samu sabbin mabiya domin su saurari wakokin su.
3. Twitter
Daya daga cikin dandalin sada zumunci wanda yayi fice wurin isar da wakoki kai tsaye ga masoya shine shafin na Twitter. Ta wannan shafin, mawaki zai iya saka wakar sa domin yada ta ga masoyan sata hanyar yin tiwitin sannan mawaki zai iya saurarar wakokin wasu gwanayen ko kuwa ka kulla alaka dasu domin su ma su yada wakar ka ta hanyar tiwitin wakar taka. Kowa zasu iya ganin wakar ka saban zasu iya latsar alamar ta "like", zasu iya barin ra'ayin su game da wakar, zasu iya ritiwitin domin ya kara kai wa fa su nasu mabiyan domin ta kara yaduwa.
4. Instagram
Wannan wata kafa ce wanda ake amfani da ita wurin baza ayuka. Idan har barci kake, ya kamata ka farka daga barcin ka saboda wannan dandalin yana tattare ne da dammammaki wanda zaka iya amfani dasu wajen yada ayukan ka ga duniya musamman ga shi mawaki.
Kar ka damu da cewa ba ka da mabiya dayawa domin kuwa dandalin sun tanadar maka da hanya mafi saukin da zaka iya tallata wakar ka ga miliyoyin mabiya a duniya ta hanyar Instagram ads. Iya kudin ka, iya shagalin ka.
5. Snapchat
Duba sa cewa wannan dandalin yana da gajeren lokaci wurin isar da sakkoni cikin awanni 24, bai kamata a ce ka munta da wannan shafin sada zumunci na Snapchat ba. Wannan kafa na da gurbin da zaka iya raba link na wakokin ka ta shafin stories, wani abun da Instagram suke da matukar rowa da shi wanda sai kana da mabiya dubu goma ko an tabbatar da shafin naka zaka ita samun daman amfani da wannan gurbin na musamman.
Ta wani hanyar na "Spotlight feature", za ka iya raba ayukan ka a kan shafin ka wanda zai iya jimawa har sai lokacin da ka ga daman canzawa. Wannan gurbin na Spotlite feature zai baka daman samun daman mutane su gan ayukan ka sannan su taimaka ma wurin kara yada ayukan ka ga duniya.
6. TikTok
Bayan shekaru kusan biyar da kafa wannan dandalin, TikTok ya kara bunkasa da mabiya masu dumbin yawa sosai. Akwai hanyoyi da dama wanda zaka iya amfani da shi wurin tallata ayukan ka domin duniya su gani a cikin sauki.
kara karantawa: 6 Best Social Media Platforms to Promote Your Music in 2021
Leave your comment