Morell ya saki kundin fefen Mansa

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Morell ya saki sabon kundin fefen MANSA. Kundin fefen dai ya sake ta ne bayan ya dau tsawon lokaci wurin tallata sunan kundin. MANSA na kunshe ne da wakoki goma sha biyar. 

Daga cikin mawakan da ya gayyatawa cikin aikin sune Ceeza Milli, Ice Prince, DJ AB, BOC, Kheengz, Kirani Ayat, Fantimoti da Abbey Lakew. 

Gwamnati ta gaggauta daukan mataki, inji mawakan arewacin Najeriya

Morell dai yayi ayuka da dama cikin kundin da masu sarrafa kida irin su TKlex, Yubskii, Presto, Omoitswavy da dai sauran su. Morell dai ya dau tsawon lokaci yana sakin wakoki a mazaunin "singles" amma wannan shine za a iya cewa karo na farko da zai saki kundin fefe bayan yawan shekarun da ya dauka yana gwagwarmaya cikin harkar waka. 

Kamun sakin kundin fefen, Morell ya saki daya daga cikin wakar dake kunshe cikin kundin mai taken Mulki. Mulki waka ce wanda ya sake ta domin ya janyo ra'ayin masoyan sa sannan kuwa ya tunasar da mawaka cewa shine dai a kan mulki idan aka zo fannin waka. 

Ko da dai akwai waka guda wanda bai sake ta ba a cikin jerin wakokin sa mai taken Arziki. Masoyansa sun tambaye shi me yasa bai sake ta ba sai yace zai sake ta nan gaba cikin "deluxe version" ma'ana fefe na musamman mai kunshe da sabin wakoki. 

Bmeri Aboki zai saki bidiyon wakar All Eyes On Me

Kundin fefen MANSA wanda Morell dai ya saka ya janyo yabo daga masoyansa daban daban. Wannan alamu ne na cewa tabbas kundin zai yi tasiri a wannan lokacin da ake samun cigaba a cikin harkar waka musamman daga bangaren Arewacin Najerya wanda tuni aka yi musu nisa a harkar saboda karancin tallafi ga mawaka da inganta sana'ar su.

Leave your comment