Gwamnati ta gaggauta daukan mataki, inji mawakan arewacin Najeriya

Photo credit: Instagram

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Mawakan arewa sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan kisan gilla da aka yi wa wasu matafiye daga jihar kudancin Najeriya wanda suke kan hanyan komawa a jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa an kashe kimanin mutane 20 wadanda duk musulmai ne wadanda suka bar jihar Bauchi bayyan sun kai ziyara daga kudancin kasar a ranar Asabar, 14 ga watan Agusta. 

Mawaka da jamma'a da dama sunyi Allah wadai da irin wannan halin duba da ire-iren hotunan da suke ta yawo a kan dandalin sada zumunci. Wannan ne ya sa mawaka irin su Larabeey ya fito ya bayyana bakin cikin sa game da wannan lamarin. Ya ce "Ba zan iya zama ina kallo ban bayyana bacin rai na game da  yanda wasu yan tsiraru suke kashe  yan uwan mu musulmai a jihar Plateau a Najeriya ba, musamman yau a hanyar Rukuba. Abun bakin ciki shine babu wani daga bangaren gwamnati da ya fito domin yin bayyani game da faruwan hakan. Sannan mun yi gum kaman bamu san da abun dake faruwa ba. Wai me ke faruwa ne? Wai meyasa duk abubuwan dake faruwa ba ma iya magana?" 

Bmeri Aboki zai saki bidiyon wakar All Eyes On Me

DJ Abba shima ya bayyana alhinin sa game da lamarin bayan da ya rubuta a shafin sa cewa "an kashe matafiya a hanyar Jos wadanda basu ji ba, basu gani ba. A nuna mana adalci". 

Umar M Shareef shima ya nuna bakin cikin sa game da lamarin bayan da ya rubuta a kan shafin sa na sada zumunci "muna kira ga gwamnati ta dauki matakin gaggawa kan wannan kisan gilla". 

Mawakin da ludayin sa ke kan dawo a jihar mai sunan Bash Ne Pha shima ya bayyana rashin jin dadin sa bayyan da ya rawaito a kan shafin sa game da yanda lamarin ya ki ci, ya ki cinyewa a jihar. Ya ke cewa "Gashi an fada toh mu gani a aikace. An dade ana kashe mu a Rukuba road. Akwai lokacin da musulmai suka je sallar idi aka kashe su  aka ce za adauki mataki ammababu matakin da aka dauka. A kwanakin nan ma, haka suka kara kase mu a wurin (Rukuba road)  amma ba a dauki mataki ba. Banda kashe masu keke napep da wadanda suka zo cirani, sai gashi jiya sun kara kashean uwa musulmai. Wani lokacin sai na dinga tunanin anya muna da gwamnati kuwa? Toh gaskiya hakurin mu ya kare. A gaggauta daukan mataki. Jinin musulmai ba jinin dabba bane". 

Chizo 1 Germany wanda shima mawaki ne amma yana zama a kasar ta Jamus ya tofa albarkacin bakin sa game da lamarin a yayin da yayi dogon jawabi kan abubuwan dake faruwa a cikin gida nan Najeriya. Ya ce "Muna mika ta'aziyya ga 'yan uwa da iyayen wanda rikicin Jos ya ritsa dasu, tare da fatan Ubangiji ya basu hakurin rashi, su kuma wanda suka mutu Allah ya gafarta musu.

Scion da Yangaboii ya gayyace BOC, DJ AB, Sojaboy, Blaqshyne da DijayCinch wurin aikin bidiyon sa

Ya cigaba da cewa "Lallai ya isa abun takaici agurin kowanne dan adam mai cikakken hankali, akan abubuwan da suke faruwa a Arewacin kasar nan, abun tambayar anan shi ne wai wanne zunubi mukayi da ake kashemu, wanne laifi mukayi da muka cancanci kisa?, kawai don mu musulmai ne?, dan mun kadaita Allah daya ne?, bamu hana kowa imaninsa ba, mai yasa mune ake son a hanamu namu." 

Chizo 1 Grrmany ya cigaba da cewa "yakamata shuwagabanin kasar nan su farka daga dogon baccin da suke su daukar mana mataki, tun kafin mu gama gamsuwa da cewa basu da amfani, muna gudun fitina ta afku wadda su kansu bazasu iya maganinta ba, mulkin da Allah ya basu badon su azurta kansu da yayansu ya basu ba, ya basu ne dansu sauke nauyin daya dora a kansu, kuma wallahi zasu bada bahasi ba musulmi ba, ba Christian ba kowaye saiya amsa tambayoyin yanda ya gabatar da mulkinsa." 

Daga karshe, Chizo 1 Germany yace "Lallai muna kira ga hukumomin wannan kasar suyi duk abunda zasuyi dan daukar mataki akan wanda sukayi wannan abun, kama daga dauri, hanasu duk wani jindadi daga dukiyar wannan kasa don sakamakon abunda sukayi....".

Leave your comment