Scion da Yangaboii ya gayyace BOC, DJ AB, Sojaboy, Blaqshyne da DijayCinch wurin aikin bidiyon sa

Photo credit: Scion da Yangaboii/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A cikin kwanakin nan Scion da Yangaboi ya wallafa wasu hotuna a kan shafin sa da ke nuna alamun cewa yana shirin sakin wani aiki. 

Hotunan wanda ya Scion da Yangaboii ya wallafa ya nuno shi tare da wasu shahararun mawaka irin su BOC Madaki, DJ AB, Dijay Cinch, Sojaboy,  Blaqshyne da BSwags. Ko da dai bamu san ko mawakan da a gayyata cikin wannan aikin suna da gurbi cikin wakar ba, amma alamu na nunin cewa akwai BOC Madaki cikin wannan aikin da za a saki.

Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka

Bayan da ya rubuta cewa "gwanaye basa damuwa da abubuwan duniya", ya ambato sunan Melas, mai daukan hoto mai motsi.

Scion da Yangaboii bai ambato sunan wakar da yake aiki a kan sa ba amma ya wallafa wani gajeren bidiyo a shafin sa na tiktok inda yake cewa "idan kuna kishi, toh ba wani riba". 

Scion da Yangaboii a baya ya saki wakar Bara Fa Suke wanda ya yayi gamayya tare da Classiq. 

Leave your comment