Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka

Photo Credit: QRY Global Concept 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Hanyar da wadanda suke da sha’awar zaman manajoji a harkar zasubi wajen tafiyar da harkokin mawaka musamman masu salon rap. Manajojin mawaka ya kamata su kokarta wajen ganin cewa sun samu record labels wanda ya dace dasu, sannan su kokarta wajen ganin cewa sun samu daukaka a cikin masana’antar a mazaunin gwanaye. 

Hanyoyi masu fiko tare da ilimi da kwarewa, hatta da sanin ya kamata abubuwa ne da kan taimaki manajojin mawaka wajen fitowa da nasarori a cikin harkokin su. Idan har so kake ka zama manajan mawaki har ka samu nasara a tattare da kai, ga hanyar da ya kamata ka dauka. 

ILIMI
Ya kamata ka nemi ilimin tafiyar da harkokin waka ta fannin me ke yayi a wannan lokacin da kuma wane irin hada-hada ke gudana a cikin masana’antar. Sannan ya kamata a ce kana da kunnuwar sauraran sauti cikin natsuwada kuma samun karatun hada-hada wanda ya shafi siya da sayarwa na wakoki da dangin su. Wannan ilimin za ka iya samun su wajen cudanya da mutane da harkoki na yau da kullum amma mafi sauki shine ka samu makarantar da ake koyar da wadannan abubuwa domin ka samu zurfin ilimin harkar da kuma yanda za ka iya takura matsaloli ko kalubalen harkar a nan gaba.  Zama ko aiki a karkashin kamfanoni dake tafiyar da ire-iren harkokin da ya shafi wakoki kan taimaka kwarai da gaskiye wajen kara kaifin basirar wanda ke sha’awar zaman manaja. 

SANAYYA
Hanyar da ta fi tasiri wajen ganin ka shigo da sabon mawaki cikin masana’antar waka shine samun kyakyawar alaka da sanayya da wadanda suke da alaka da harkar daga tushe. Ire-iren su suna da tasiri domin a lokacin da kake a mazaunin manaja mai tasowa, ya kamata ka wanke tukunyar ka domin tuwon gobe da manyar dake cikin harakar. Ka samu kyakyawar fahimta da wadanda ake damawa dasu a cikin masana’antar, sannan ka dinga lura da abubuwan da ke tafiye a masana’antar ta hanyar kaffafan sadarwa ta zumunci, waya da manajojin gidajen wassani, masu farautar basira wato talent managers, gwanayen mawaka da kuma manyan manajojin record label. Ka yawaita ziyarar wurarren wassani, taron bita, studio, taron shawarwari da dai sauran su domin samun daman haduwa da massana da abokan hurda. Ta nan ne zaka san su wa suka fi son irin salon wakoki na hausa hiphop, hausa rap, ingausa, afro-pop da dai sauran su. 

Iya Gane Gwanaye A Duhu
Hanyar sadawa na zamani shine hanya mafi saukin da za ka iya samun mawaka masu basira a saukake. Akwai mawakan salon rap wadanda sun yi fice a kan kafaffen sada zumunci a inda sukan saki bidiyoyin su a shafukan su Kaman su youtube, facebook, instagram, twitter da dai sauran su. Za ka iya tuntubar su idan sun bar lambobin wayar su ko kuma ka tura sako ta email. Daga nan kuwa zaka iya gina alaka mai daurewa tsakin kai da mawakin har ta kai ga gacin da z aka iya zama manajan sa. A mazaunin manaja, ya kamata ka yawaita barin sakonni a kan shafin sa masu kunshe da irin kokarin da yake da kuma yanda zai kara kaimi a aiyukan sa. Kar ka manta da cewa zaka iya ziyartar  wassanin shi mawakin domin ka karanci yanda yake aiwatar da ayukan sa a kan dandali da kuma irin baiwar da Allah yayi masa da irin alakar dake tare da shi da masoyan sa, sannan ka mara masa baya.
Za ka iya gabbatar da takardun contragi ga shi mawakin idan kun kulla alaka mai daurewa tsakanin ku. Bayan ya sa hannu, sai ka shirya masa hanyar da zai hadu da manyan kusoshin masana’antar, wassani da kuma yanda zai siyar da ayukan sa ga duniya. 

Ka bunkasa masu aiki a karkashin ka
A yayin da mawakan dake karkashin ka suka fara samun nasara a harkokin su, ayukan ka tabbas zasu karu. Tsara jadawalin ayukan mawakin yak an zo da dawainiyya dayawa. A kan samu albazaranci da kudadden shiga sabo da yawaitar su, sannan harkoki tareda lauyoyi yana da matukar muhimmanci. Ka yi amfani da alakar dake tsakanin kai da ma’aikata irin su booking managers, wakilai da masu bada shawarwari ga mawakin dake karkashin ka. Alhakin ka ne ka nemi irin wadannan ma’aikata saboda ka aiwatar da ayukan ka cikin tsari da masana. 

KA GINA MARTABAR KA
Mudin kana da mawaka daya zuwa biyu a karkashin kulawarka, matakin gaba shine ka gina martabar ka a mazaunin manajan da ba ya wasa da harkokin sa a cikin masana’antar. Manajojin da suka yi fice a harkar suna da fayil na mawakan da suka taba aiki dasu a kan yanar gizo da kuma a rubuce cikin littafi na musamman. 

GINA YANAR GIZO
Ka gina yanar gizo na musamman domin tallata manhajar ka ga duniya tare da adireshin ka lambobi na musamman da za a iya tuntubar ka, sannan da tsarin da mawaka zasu bi wajen mika ayukan su domin samun tantacewa na musamman daga gare ka.
A kwana a tashi, mawaka zasu mika ayukan su gare ka domin ka zama manajan su a nan gaba saboda ficen ka a cikin masana’antar ta waka.

Leave your comment