Bmeri Aboki zai saki bidiyon wakar All Eyes On Me

Photo credit: Bmeri Aboki/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Bmeri aboki shahararen mawakin salon Hip-hop ne dake zaune a jihar Lagos a Najeriya.  Haifaffen unguwar Agege, Bmeri Aboki ya zamo gwani a fagen zuba wanda ya janyo masoyansa da yan unguwar Agege suke masa lakabi da sunan aboki. 

Larabeey ya ce ya samu cigaba a harkokin rayuwa

Bmeri Aboki ya saki wakoki da dama a karkashin label dinsa mai cin gashin kansa wanda ya saka mata suna da BMA Entertainment. Kamun ya bude label din sa, ya yi aiki karkashin label na tsohon mawakin salon hiphop Eedrees Abdulkareem mai sunan LaKareem Records. 

Bmeri Aboki ya bar label din LaKareem Records bayan da yarjejeniyar dake tsakanin su ta zo karshe.
Bmeri Aboki ya saki kundin fefen sa a karo na biyu mai taken Mele wanda ke kunshe da wakoki 15. Wakokin da suka yi fice a kundin su ne Jini, Mele da Freestyle session. Yanzu dai yana shirin fitar da sabuwar aiki cikin kundin mai taken All eyes on me. 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Wakar "All eyes on me" ya gayyaci mawaki Komandah cikin aikin. Ya bayyana zai saki aikin ne kan shafin sa na Instagram. Ya rubuta cewa "tabbas sau dayawa kun ci karo da wadannan kalmomin na all eyes on me shiyasa muka ce bari mu kara kayata shi. Ku sha kurumin ku domin zamu saki sabon bidiyo" 

Leave your comment