Larabeey ya ce ya samu cigaba a harkokin rayuwa

Photo credit: Larabeey/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Larabeey daya ne daga cikin mawakan arewacin Najeriya wanda tauraron sa ke haskawa yanzu. Mawakin dan asalin jihar Bauchi ya shahara ne ta bangaren rera wakoki irin na salon Hip-hop da Afro-pop. 

Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka

Larabeey ya saki wakoki da dama sannan ire-iren wakokin da ya kan saka, suna fitowa ne hade da bidiyoyi. A halin yanzu dai, akwai wani sabon aikin da ya saka mai sunan "I'm a star". 

Mun tuntube shi domin jin ra'ayin sa game da fito da wannan aikin ya ce " Na yi wakar I'm a star domin mutane su san yanda abubuwa na suka kasance yanzu. Akwai bambanci da da tunda a baya akwai abubuwan da suka gagare mu amma yanzu an samu bambancin. Wajen da muka kasa shiga a da, yanzu a saukake muna iya shiga. Abubuwan da mukan kasa yi, yanzu muna yin su." 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Da ga karshe yace "A takaice dai yanzu an samu cigaba a harkokin rayuwa gaba daya".

Leave your comment