Nomiis Gee da Ricqy Ultra sun saki bidiyon Anzo Wurin

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Hamshaken mawakan da sukayi shura a fannin wakar hiphop a arewacin Najeriya, Nomiis Gee da Ricqy Ultra sun saki bidiyon wakar su mai taken Anzo Wurin. 

Watani baya sun dan saki somin tabi na gajeruwar bidiyon domin masoya su san da cewa aikin na dab da fitowa. Yanzu dai sun cika alkawarin su. 

Hanyoyi Shida Da Zasu Taimaka Ma Wajen Zama Manaja Na Kwarai A Masana'antar Waka

A cikin bidiyon dai sun gayyaci shahararen mai sarrafa kida mai sunan DJ Kool Babs tare da yan rawan zamani irin su Kinah AK da tawagar sa. Banda su kuwa, akwai yan wasan fina-finan Kannywood irin su TK Guy na Dadin Kowa, IB da Rambo da dai sauran su. 

Anzo Wurin  waka ce mai nishadantarwa sannan akwai hasashen cewa aikin zai kara darajar bidiyoyin da ke fitowa daga wannan sashi na Najeriya. 

Nomiis Gee ya halarci wasan motoci wanda Dark Knight Motor Sports suka gudanar a Kano

Ricqy Ultra ya dan saki jawabi game da aikin a lokacin da ya rawaito a shafin Instagram din sa cewa "sarrafa bidiyoyi musamman na waka yana bukatan shirye-shirye da aiwatarwa. Sannan kuwa sai mutum ya tsaya da kafafuwan sa wajen ganin an samu nasara. Alhamdulillah mun kammala aikin kuma ina matukar farin ciki da ganin cewa mun saki aikin ga masoyan mu." 

Daga karshe ya ce "Insha Allah, aikin zai buda mana wasu hanyoyin da zasu zamo mana mafi alkhairi."

Leave your comment